Cote d'Ivoire

Baza ayi zabe cikin lafiya ba - Gbagbo

Laurent Gbagbo tsohon Shugaban Cote D'Ivoire
Laurent Gbagbo tsohon Shugaban Cote D'Ivoire Jerry Lampen/Pool via REUTERS

Tsohon Shugaban kasar Cote d’Ivoire Laurent Gbagbo ya bayyana cewar zaben shugaban kasar da zai gudana a karshen wannan mako zai haifarwa kasar mummunar rikici, inda ya bukaci tattaunawa.A hirar sa ta farko da tashar TV5 Monde, Gbagbo yayi hasashen cewar kasar na fuskantar bala’I, kuma dalilin da yake Magana akai kenan.

Talla

A daya geffen ,kakkakin yan Adawa Pascala Affi Guessa ya bayyana matsayin su,ya kuma bukaci Shugaban kasar Alassane Dramane Ouattara  da ya saurari koken yan kasar mudin ya na fatan cira da mutunci sa da kuma kauce sake jeffa kasar cikin wani yanayi na rashin tabbas bayan zabe.Kakakin Jam’iyyun adawar Cote d’Ivoire, Pascal Affi-Nguessen yayi watsi da zaben a hira ta musamman da RFI da kuma France 24.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.