Afrika

Shugaban Algeria na cikin yanayi mai kyau

Gwamnatin Algeria ta sanar da cewar shugaban kasa Abdelmajid Tebboune da aka ruga da shi zuwa asibiti a kasar Jamus na cikin yanayi mai kyau.

Abdelmadjid Tebboune, Shugaban Algeria
Abdelmadjid Tebboune, Shugaban Algeria Toufik Doudou/AP Photo
Talla

Ofishin shugaban yace an yiwa shugaban gwajin kuma sakamakon ya nuna cewar baya cikin hadari, yayin da ake cigaba da kula da lafiyar sa.

An dauki Tebboune zuwa Jamus ne bayan killace kan sa a asibitin sojin dake Algiers saboda bayan wasu daga cikin jami’an sa sun kamu da cutar korona.

Da kama shugabancin kasar shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune ya sha alwashin bayar da cikakkiyar dama ga matasan da ke zanga-zangar neman sauyi wajen ganin sun shigo don a dama da su wajen ciyar da kasar gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI