Shugaban Hukumar CAF ya kamu da coronavirus

Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Afirka CAF, Ahmad Ahmad
Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Afirka CAF, Ahmad Ahmad france24.com

Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Afirka, CAF, Ahmad Ahmad, ya kamu da annobar COVID-19.

Talla

Labarin na kunshe ne a cikin wata sanarwa a shafin intanet na hukumar kwallon kafar nahiyar .

Sanarwar ta ce, Ahmad ya nuna almun cutar ne, bayan isar Alkahiran Masar a ranar 28 ga watan nan na Oktoba, abin da yasa akayi masa gwaji, kuma aka tabbatar ya kamu da cutar, kuma yanzu haka ya killace kansa a wani Otel na tsawon kwanki 14.

Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da shugaban ya nuna aniyar sake neman wa'adi na biyu a jagorancin Hukumar Kwallon Kafar Afirka, bayan da kasar sa Madagascar ta amince ya ci gaba da wakilcin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.