Coronavirus

Corona ta harbi mutane 170 cikin kwana 1 a Najeriya

Wani ma'aikacin lafiya yana daukar  samfurin gwajin cutar corona daga wani mara lafiya.
Wani ma'aikacin lafiya yana daukar samfurin gwajin cutar corona daga wani mara lafiya. AFP

A Najeriya, mutane 170 ne hukumomi suka sanar sun harbu da cutar Coronavirus daren Juma’a, abin da ya kawo adadin wadanda cutar ta harba zuwa dubu 62 da dari 6 da 91, mako na 13 a jere da adadin wadanda wannan cuta ta kama ke zuwa kasa da dari 3.

Talla

Sai dai an samu mutane 3 da cutar ta kashe, lamarin da ya kai adadin mamata zuwa dubu 1 da dari da 44, kamar yadda alkalumman hukumar yaki da cututtuka ta kasar ya nuna.

A cikin makonni 2 da suka wuce, adadin wadanda cutar ta aika barzahun sun kasance a kasa da 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.