Turai

Cutar Korona zata sa a sake killace Ingila

Firaministan Birtaniya Boris Johnson
Firaministan Birtaniya Boris Johnson REUTERS/Toby Melville/Pool

Firaministan Birtaniya Boris Johnson na tunanin sake kakaba dokar takaita zirga zirga a fadin kasar a cikin kwanaki masu zuwa sakamakon sake dawowar cutar korona ganin yadda matakan da ya dauka yanzu haka suka gaza aiki.

Talla

Ana saran Johnson ya bayyana sabbin matakn ranar litinin mai zuwa, wadannan zasu shafi rufe daukacin shagunan sayar da kayayyaki, amma dokar ba zata shafi makarantu kanana da manya ba.

Jaridar The Times ta kasar tace dokar wadda ake saran ta fara aiki daga ranar laraba mai zuwa zata dore har zuwa ranar 1 ga watan Disamba.

Ana saran Firaministan yayi amfani da karshen makon nan wajen tattaunawa da manyan jami’an sa dangane da daukar sabbin matakan, ciki harda gudanar da taron Majalisar ministoci gobe lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.