Afrika

Gwamnatin Nijar tace an saki Ba'Amurken da aka sace

Yankin jihar Tahoua  a Jamhuriyar Nijar
Yankin jihar Tahoua a Jamhuriyar Nijar Pauline Maucort

Gwamantin Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewar an kubutar da  Ba'Amurken da aka sace a Massalata dake Yankin N'Konni a cikin wannan mako.

Talla

Ministan tsaron kasar Issoufou Katambe ya tabbatar da sakin Philip Walton daren jiya juma’a, ba tare da Karin bayani kan yadda aka kubutar da shi ba.

Tashar talabijin din ABC dake Amurka tace zaratan sojojin Amurka da taimakon takwarorin su na Najeriya da Nijar suka kubutar da Walton a wani yankin Najeriya bayan sun kashe Yan bindiga 6 daga cikin 7 da suka yi garkuwa da shi.

Jonathan Hoffman, babban kakakin ma’aikatar tsaron Amurka yace dakarun sojin sun kaddamar da farautar Walton ne yau da sassafe, kuma sun samu nasara ba tare da wani ya jikkata ba.

Jami’in ya yabawa abokan aikin su dake Najeriya da Nijar wajen nasarar da aka samu na kubutar da Walton daga hannun Yan bindigar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI