Cote d'Ivoire

Jama'a sun soma kada kuri'ar su a Cote D'Ivoire

Wasu daga cikin magoya bayan Shugaban kasar kuma dan takara Alassane Dramane Ouattara
Wasu daga cikin magoya bayan Shugaban kasar kuma dan takara Alassane Dramane Ouattara Issouf SANOGO / AFP

A yau asabar ake gudanar da zaben shugabancin kasar Cote d’Ivoire, a dai dai lokacin da dubban jama’a suka soma kauracewa birnin Abidjan sabili da matsalar tsaro.

Talla

A jajuburin zaben an fuskanci tashin hankali a wasu biranen kasar ta Cote D’Ivoire,a dai-dai lokacin da sakatary Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres ta bakin kakkakin sa Stephane Dujarric ya bukaci yan siyasar kasar da su kai zuciya nisa, kazzalika babban jami’in na hukumar turai Josep Borreli ya ce kungiyar Turai na fatan kowane daga cikin yan siyasa na Cote D’Ivoire zai taka gaggarumar rawa don tabbatar da kwanciyar hankali a wannan lokaci mai muhimanci.

Matakin Shugaban kasar kuma dan takara Alassane Ouattara na sake neman wa’adi na uku ya haifar da rudani a fagen siyasar wannan kasa,takanas yan adawa suka gayyaci magoya bayan su da su kauracewa zaben ga baki daya.

Ministan tsaron kasar Cote D’Ivoire ya dau alkawali na tabbatar da tasro da kuma kare farraren hula a wannan lokacin zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.