Amurka

Obama da Biden zasu hadu a gangamin Pensylvannia

Dan takara Donald Trump da Joe Biden na jam'iyyar Democrat a lokacin muhawara
Dan takara Donald Trump da Joe Biden na jam'iyyar Democrat a lokacin muhawara Jim Bourg/Pool via AP

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama zai halarci taron gangamin yakin neman zaben tsohon mataimakin sa Joe Biden wanda ke fafatawa da shugaba Donald Trump a zaben da za’ayi ranar 3 ga watan gobe. A yau Asabar mutane kimanin milyan 86 ne suka kada kuri'u su daga cikin mutane milyan 230.

Talla

Wannan zai zama karo na farko tun bayan fara yakin neman zaben da Obama zai halarci gangami tare da Biden wanda za’a yi a  Pennsylvannia.

Rahotanni sun ce zasu jagoranci jerin gwanon motoci da kuma gangami a biranen Flint da Detroit dake Michigan, inda ake saran fitaccen mawakin Amurka Steve Wonder zai rera waka a taron.

A zaben shekarar 2016 shugaba Donald Trump ya samu nasara a Jihar da kasa da kashi biyu kan Hillary Clinton, amma kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewar Biden na gaba da Trump da kashi 7.

Shima shugaba Trump wanda ya soki gangamin da Obama keyi cewar baya tara yawan mutane kamar na shi, yau zai ziyarci Pennsylvaniar inda zai jagoranci gangami guda 3.

Rahotanni sun ce yanzu haka Amurkawa sama da miliyan 80 sun riga sun kada kuri’un su, cikin su harda shugaba Donald Trump da dan takarar Democrat Joe Biden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.