Turai

Sean Connery ya rasu ya na mai shekaru 90

Sean Connery dan wasan fina-fiani da yayi suna a James Bond
Sean Connery dan wasan fina-fiani da yayi suna a James Bond C.C 3.0/Stuart Crawford

Fitaccen mai shirin fina finan Birtaniya da yayi suna a shirin fim din James Bond Sean Connery ya rasu yau yana da shekaru 90 a duniya.

Talla

Connery da ya samu lambar girmar Sarauniyar Ingila a shekara ta 2000 ya lashe kyaututtuka da dama a rayuwar sa bayan kwashe shekaru yana taka rawa a shirin fina finai, kuma daga cikin kyaututtukan harda Golden Gloves sau 3 da Kyautar Bafta sau 2.

Daga cikin fina finan da suka daga darajar Connery harda ‘Indiana Jones’ da ‘The Rock’ da ‘The Hunt for Red October’ da ‘The Last Crusade’.

Masu sharhi kan shirin fina finai sun bayyana shi a matsayin mafi kwarewa daga cikin gwarzayen da suka fito a shirin fina finan James Bond ko kuma 007.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.