Saudiya

Yan Sanda sun kama mutumin da ya kutsa kai da mota Masallachin Ka'aba

Babban Masallacin Makkah
Babban Masallacin Makkah AFP

Hukumomin kasar Saudi Arabia sun tabbatar da kama wani mutuum da ya kutsa da mota cikin Masallachin Makkah ranar juma’a da daddare.

Talla

Kafofin yada labaran kasar sun ce direbar motar da ba bayyana ko waye ba ya afkawa shingen da aka saka a Masallachin Ka’aba inda ya shiga cikin inda ake gudanar da ibadar dawafi.

Sanarwar tace yanzu haka mutumin wanda ake zaton bashi da cikakken hankali na tsare a wajen jami’an tsaro, kuma an tabbatar da cewar dan kasar Saudi Arabia ne.

Masallachin Ka’aba shine mafi daraja ga al’ummar Musulmin Duniya, wanda ibada a cikin sa ya zarce an kowanne Masallachi dake doron kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.