Faransa

A kwantar da hankali-Ouattara

Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara kwana daya bayan zaben kasar, ya na kira ga yan kasar na ganin sun kwantar da hankula bayan zaben da aka gudanar jiya a kasar wanda abokan hamayya suka yi watsi da shi a matsayin mara inganci, bayan kauracewa da kuma zanga zanga a wasu sassan kasar.

Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara.
Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara. REUTERS/Luc Gnago/File Photo
Talla

Akalla mutane 30 ne suka mutu a rikice rikicen gabanin zabe tun daga watan Agusta, abin da ya sa ake fargabar sake dawowar irin tashin hankalin da ya yi sanadin mutuwar mutane dubu 3 shekaru 10 da suka wuce, lokacin da tsohon shugaba Laurent Gbagbo ya ki sauka daga karagar mulki duk da shan kayen da ya yi a zabe.

A waje daya kuma, tsohon jagooran ‘yan adawan Ivory Coast Guillaume Soro, wanda hukumomin kasar suka haramta mai tsayawa takara ya ce daga yanzu ya daina daukar Alassane Ouattara a matsayin shugaban kasa, yana mai kira ga ‘yan Ivory Coast da su yunkuro don kifar da gwamnatinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI