Najeriya

Ba za mu tilasta wa jami'an mu komawa aiki ba - Hukumar 'yan sandan Najeriya

Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu NAN

Hukumar kula harkokin ‘yan sanda a Najeriya ta ce ba za ta tilasta wa duk wani jami’in dan sanda komawa bakin aiki ba.

Talla

Hukumar tana mayar da martani ne ga rahotannin da ke cewa ta yi barazanar sallamar duk jami’in dan sandan da bai koma bakin aiki ba, a wata sanarwa da ta fitar a yau Lahadi.

Hukumar ta ce babu gaskiya a rahotannin da wasu kafafen yada labarai suka watsa, tana mai cewa zai kasance rashin sanin yakamata idan ta sallami jami’in dan sanda da ya gaza komawa bakin aiki.

Kafofin yada labarai a ciki da wajen Najeriya sun kawo rahoton yadda zanga zangar lumana ta rikide zuwa tarzoma bayan zargin cewa sojoji sun bude wa masu zanga zzanga wuta a Lekki da ke jihar Legas.

Fiye da jami’an ‘yan sanda 20 aka kashe a wannan tarzoma, bayan da ‘yan daba suka yi ta farautar masu kayan sarki, suna kuma cinna wa ofisoshin ‘yan sanda wuta.

Tuni jami’an ‘yan sanda da dama suka yi watsi da wuraren aikinsu biyo bayan farautarsu da ‘yan daba ke yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.