Faransa

Gwamnatin Faransa ba ta goyon bayan batanci ba ga Musulunci -Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Christian Hartmann/Illustration

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a wata tattaunawa da gidan talabijen na Al Jazzira, ya bayyana cewa ko kadan manufar sa ,ba ita ce ta haifar da bacin rai,ko janyo rikici tsakanin Faransa da kasashen musulmai ,aminan Faransa.

Talla

Shugaban ya bayyana cewa manufar sa a matsayin Shugaban kasa, nauyi ya hau kan sa don kare muradun kasar,da kuma baiwa kowa inci fadar albarkacin bakin sa, ko kadan gwamnati ba ta da hannu a batun zane-zane,jaridar Charlie Hebdo na zaman kan ta,kamar sauren kaffofin yada labaran Faransa.

Shugaban ya jaddada aniyar hukumomin kasar na mutunta addini musulunci.

Faransa za ta tura jakadan ta Turkiya a yau Lahadi, wanda zai kuma samun tattaunawa da hukumomin kasar kamar dai yada ministan harakokin wajen kasar Jean Yves Ledrian ya sanar.

Gwamnatin Faransa ba ta goyi bayan batanci ga musulunci-Macron

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.