Najeriya

Najeriya: 'Yan bindiga sun kashe mutane 13 a Zamfara

A Najeriya, ‘yan bindiga masu satar shanu sun kashe mutane 13 a wani kauye dake jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya a yammacin jiya Asabar.

Irin bindigogi samfurin AK 47 da 'yan bindiga ke amfani da su a sassan arewacin Najeriya.
Irin bindigogi samfurin AK 47 da 'yan bindiga ke amfani da su a sassan arewacin Najeriya. RFI Hausa
Talla

‘Yan bindigar sun afka wa kauyen Kadamutsa dake karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara ne da misalin karfe 3 na rana, kuma suka ci Karen su ba babbaka na fiye da sa’o’i 2, kamar yadda wata majiya a yankin ta shaida wa RFI Hausa.

Majiyar ta ce maharan sun kwashe wannan tsawon lokaci suna dibar shanu da sauran dabbobi tare da harbin mutane ba tare da wani dauki daga jami’an tsaro ba.

Majiyar ta ci gaba da cewa wasu daga cikin mutane 13 da ‘yan bindigar suka kashe ‘yan banga ne da suka kai gudummawa daga kauyukan dake makwaftaka da kauyen Kadamutsa.

Wannan harin na zuwa ne duk da sulhun da gwamnatin jihar ta Zamfara ta ce ta yi da ‘yan bindigar.

Al’ummomi a yankuna da daman a arewacin Najeriya sun shiga cikin mawuyacin hali sakamakon kisan gillar da wadannan ‘yan bindida suke musu a kai a kai.

Ko a cikin makon da ya gabata, an samu rahotanni akan hare haren ‘yan bindiga a kauyuka kusan biyar na jihar Zamfara.

Wannan lamari ya hana al’ummomin da abin ya shafa yin noma saboda tsoron zuwa gonakinsu, abin da ya sa manazarta ke ganin zai haddasa matsalar abinci a shekara mai kamawa idan ba gwamnati ta kai dauki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI