Macen da ta fi arziki a Afrika ta zama bazawara

Isabel Dos Santos, diyar tsohon shugaban Angola.
Isabel Dos Santos, diyar tsohon shugaban Angola. REUTERS/Toby Melville

Babban dan kasuwa, dan kasar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Sindika Dokolo, wanda shine miji ga hamshakiyar attajira, Isabel Dos Santos, diya ga tsohon shugaban Angola, kuma macen da ta fi arziki a nahiyar Afrika ya rasu a Dubai, sakamakon hadarin da yayi a teku yayin nunkaya.

Talla

Mutuwarsa ta zo ne a daidai lokacin da suke fuskantar kalubale ta fuskar shari’a, saboda sabon shugaban Angola, João Lourenço da ya dare karagar mulki a shekarar 2017 ya kaddamar da bincike a kansu a kan zargin cin hanci da rashawa, lamarin da ya sa aka kwace wasu daga cikin kadarorinsu.

Hukumomin Angola na zargin Isabel ne da yin kwanciyar magirbi a kan wasu damasheren kudade da suka kai dala biliyan 1 na kamfanonin danyen man fetur da na lu’u’lu’u a kasar da akasarin al’ummarta ke fama da bakin talauci.

Sindika Dokolo da Isabel Dos Santos sun musanta aikata ba daidai ba, amma bankuna a turai na kallon su a matsayin mutane masu hadari wadanda harka da su tamkar kasada ce, kamar yadda wata jaridar kasar Switzerland, Le Temps ta ruwaito.

A shekarar 1972 haifi Sindika Dokolo. Mahaifinsa dan kasuwa ne kuma mutum na farko da ya mallaki banki mai zaman kansa a kasar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, kuma ya fantama a zamanin mulkin kama - karya na Mobutu Sese Seko daga shekarar 1965 zuwa 1997. Mahaifiyarsa ‘yar kasar Denmark ce, kuma tun a shekarar 1966 take birnin Kinshaha har zuwa yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.