'Yan bindiga sun kashe mutane 32 a kasar Habasha

Sojojin Habasha
Sojojin Habasha REUTERS/Shabelle Media

Hukumar Kare Hakkin Bil Adama a kasar Habasha tace wasu Yan bindiga sun kashe fararen hula 32 a wani hari da suka kai a karshen mako a Yankin Oromia mai fama da tashin hankali.

Talla

Sanarwar da Hukumar ta gabatar yace an samu tashin hankalin ne a ranar lahadi a garin Wollega dake Yammacin kasar lokacin da tawagar Yan bindigar mai dauke da mutane akalla 60 suka kai harin kan fararen hula.

Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne kan Yan kabilar Amharic, wadanda sune kabilu na biyu mafi yawa, inda aka dinga jan su zuwa wata makaranta kafin a harbe su.

Sanarwar Hukumar yace alkaluman wadanda suka mutu ya kai 32, amma rahotanni sun ce yana iya fin haka.

Gwamnatin yankin Oromia ta zargi yayan kungiyar ‘Oromo Liberation Army’ dake dauke da makamai da aikata kisan, saboda yadda suka saba kai hari suna sace mutane da tada bam da kuma hallaka su.

Wani shaidar gani da ido ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar ya kirga gawarwaki 50 da kan sa, yayin da ba za’a rasa wasu da suka fada a daji ba.

Shugaban Hukumar kare hakkin Bil Adamar Daniel Bekele ta bukaci gwamnati ta binciki dalilin da ya sa sojoji suka bar yankin, inda yake cewa babu dalilin da zai sa aiwatar da irin wannan kisan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.