Amurka

Amurkawa sama da miliyan 99 suka kada kuri’un su a yau

Yau al’ummar kasar Amurka ke gudanar da zaben shugaban kasa, inda miliyoyin al’ummar kasar ke kada kuri’a domin ganin wanda zai samu nasara tsakanin shugaba Donald Trump mai ci daga Jam’iyyar Republican da abokin karawar sa Joe Biden daga Jam’iyyar Democrat.

Masu zabe daga bangaren Democrat
Masu zabe daga bangaren Democrat Éditions Fayard/Fondation Jean Jaurès
Talla

Miliyoyin Amurkawa ke kada kuri’u yau a zaben na Amurka wanda tuni ya dauke hankalin kasashen duniya wadanda suka zuba ido domin ganin wanda zai samu nasara tsakanin shugaba Donald Trump da ya kwashe shekaru 4 a karagar mulki da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden.

Hukumar zabe tace kafin fara zaben na yau akalla Amurkawa sama da miliyan 99 suka kada kuri’un su a jihohi daban daban domin kaucewa tururuwar jama’a wajen kada kuri’a da kuma annobar korona dake cigaba da hallaka rayuka, kuma cikin wadanda suka kada kuri’u da wuri harda shugaba Donald Trump da abokin hamayyar sa Joe Biden.

Kuri’un jin ra’ayin jama’a da dama sun nuna cewar tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden ke sahun gaba wajen lashe zaben, amma shugaba Donald Trump yace yana da fata mai kyau cewar shi zai samu nasara, kuma zai gagarumar nasarar da ba’a taba gani ba a jihohi irin su Florida da Arizona wadanda ke taka rawa wajen nuna wanda zai zama shugaban Amurka.

Joe Biden ya ce lokaci yayi da shugaba Donald Trump ya tattara kayan sa ya bar fadar shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI