Amurka

Ana gudanar da zaben Majalisar wakilai a Amurka

Yayin da ake gudanar da zaben shugaban kasar Amurka yau, haka kuma ana gudanar da zabukan kujeru 435 na Majalisar wakilai wanda ake saran Jam’iyyar Democrat ta cigaba da samun rinjayen da take da shi yanzu haka ko kuma kara yawan kujerun da take rike da su.

Wasu daga cikin yan majalisar Dattawan Amurka
Wasu daga cikin yan majalisar Dattawan Amurka REUTERS/Carlos Jasso
Talla

Daga bangaren Majalisar Dattawa kuma za’a gudanar da zaben kujeru kashi daya bisa uku na kujerun a Majalisar da Yan Republican ke da rinjaye da kujeru 53, yayin da Democrat ke da kujeru 47.

Rahotanni sun ce akwai alamun cewar Jam’iyyar Democrat na iya kwace wasu kujerun republican domin samun rinjaye a Majalisar, kuma daga cikin kujerun dake rawa akwai na shugaban masu Rinjaye Mitch McConnel da Sanata Lindsay Graham shugaban kwamitin shari'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI