Duniya

Shugabanin Duniya masu yawan shekaru

Shugabanin Duniya masu yawan shekaru
Shugabanin Duniya masu yawan shekaru RFI Hausa

Yayin da ake dakon sakamakon zaben shugaban Amurka, tsakanin shugaba Donald Trump mai shekaru 74 da Joe Biden mai shekaru 77, duniya na cigaba da samun shugabanni masu yawan shekaru dake jagorancin kasashen su.

Talla

Firaministan Malaysia Mahathir Mohammed shine shugaban duniya da yafi yawan shekaru, inda yake da shekaru 95 a duniya, sai Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu mai shekaru 94 da take rike da mukamin shugaban kasa a kasashe 16 na duniya, cikin su harda Canada da Australia.

Shugaba Raul castro na da shekaru 89 a duniya, sai shugaba Paul Biya na kasar Kamaru wanda yake da shekaru 87 a duniya, sannan shugaban Lebanon Michel Aoun mai shekaru 85 kamar shugaban Falasdinu Mahmud Abbas shima mai shekaru 85.

Sarki Salman bin Abdelaziz na Saudi Arabia na da shekaru 84, sai Shugaban Laos Bounnhang Vorachith mai shekaru 83 a duniya, sai Ayatollah Ali Khamenie na Iran mai shekaru 81, sannan kuma Nursultan Nazarbayev na kasar Kazakhstan mai shekaru 80 a duniya

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa na da shekaru 78 a duniya, sai shugaba Alpha Conde na Guinea mai shekaru 82, sannan shegaba Dennis Sassou Nguesso na Congo mai shekaru 77, kuma ya kwashe shekaru 37 a karagar mulki.

Shima shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na da shekaru 77.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.