Afrika

Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da malaman makarantu a Kamaru

Wasu yan bindiga a kasar Kamaru sun sace malaman makarantu guda 11 daga makarantar Kumba dake Yankin Yan Aware kwanaki bayan harin da aka kai wanda yayi sanadiyar kashe wasu dalibai.

Dalibai dake nuna fushin su bayan kisan wasu daliban da yan bindiga suka yi  a garin Kumba
Dalibai dake nuna fushin su bayan kisan wasu daliban da yan bindiga suka yi a garin Kumba REUTERS/Josiane Kouagheu
Talla

Rev Fonki Samuel Foba dake shugabancin makarantun dake Yankin yace ayau talata aka sace malaman a gaban daliban su.

Foba yace da farko malamai 12 aka tafi da su, daga bisani guda ya sulale ya gudu.

Ya zuwa yanzu ba’a iya tantance yan bindigar da suka aikata aika aikan ba, amma karamar hukumar yankin na zargin yan aware wadanda ke kai hare hare a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI