Habasha

Rundunar Sojin Habasha ta kaddamar da yaki kan masu rike da iko a yankin Tigray

Firaministan Habasha Abiy Ahmed.
Firaministan Habasha Abiy Ahmed. AFP/Monirul BHUIYAN

Rundunar Sojin Habasha tace ta kaddamar da yaki akan Jam’iyyar dake mulkin Yankin Tigray bayan kwashe kwanaki biyu ana musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.

Talla

Bayan kwashe sa’oi 48 ana musayar wuta tsakanin Yan bindigar dake dauke da makamai a Yankin Tigray da rundunar sojin kasar, mataimakin hafsan sojin Berhanu Jula yace kasar su ta fada cikin yanayin yakin da bata shirya ba, kuma abin kunya da rashin hankali.

Janar Berhanu yace za suyi iya bakin kokarin su wajen ganin yakin ya tsaya akan iyaka ba tare da ganin ya shigo yankin da fararen hula suke zama ba.

Firaminista Abiy Ahmed ya umurci sojojin da su kaddamar da yakin bayan kazamin harin da aka kai sansanin su.

Shugaban yankin Tigray mai cin gashin kan sa Debretsion Gebremichael ya bayyana hare haren da sojojin suka kaddamar a matsayin yunkurin mamaya, inda yace zasu cigaba da fafatawa domin kare muradun su.

Gwamnati ta kuma bayyana dokar ta baci na watanni 6 a yankin da aka katse harkokin sadarwa da intanet baki daya.

Abiy ya shaidawa al’ummar kasar cewar ya umurci sojojin kasar da su kaddamar da hare-hare domin kare kasar saboda yadda 'yan bindigar suka wuce gona da iri.

Ko a karshen mako an samu wani hari da 'yan bindigar suka kashe mutane sama da 30 a yankin Oromia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.