Anyi jana'izar dalibai da aka kashe a yankin 'yan awaren Kamaru

Dubban Mutane ne suka halarci jana’izar daliban makarantar da Yan bindiga suka hallaka a Kumba dake Yankin da ake fama da matsalar Yan aware a kasar Kamaru.

Masu zanga-zangar adawa da kissan dalibai a Kamaru
Masu zanga-zangar adawa da kissan dalibai a Kamaru REUTERS/Josiane Kouagheu
Talla

Cikin wadanda suka halarci jana’izar harda Firaministan Kamaru Joseph Dion Ngute wanda ya sha alwashin ganin jami’an tsaro sun kamo wadanda suka aikata kisan an kuma hukunta su.

A ranar 24 ga watan Oktoba ne Yan bindiga suka kai hari makarantar Mother Francisca inda suka harbe dalibai guda 7 har lahira, abinda ya gamu da mummunar suka daga ciki da wajen Kamaru.

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Afirka duk sun yi Allah wadai da harin wanda suka bayyana shi a matsayin abin takaici da kuma tada hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI