ICC ta bukaci Kenya da ta mika mata wasu mutane biyu kan zargin aikata laifukan yaki
Babbar mai gabatar da kara a Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya dake Haque Fatou Bensouda ta bukaci gwamnatin Kenya da ta mika mata mutane 2 da ake zargi da lalata shaidun da ake da su a shari’ar laifuffukan yakin da ake tuhumar wasu yan siyasar kasar, bayan wani shaida guda ya gabatar da kan sa.
Wallafawa ranar:
Wani lauyan kasar Paul Gicheru ya gabatar da kan sa ga kotun ranar litinin kuma ana saran ya gurfana a gaban alkalai domin amsa tuhuma dangane da lalata shaidun wannan juma’ar.
Za’a tuhumi Gicheru da laifin baiwa shaidu guda 6 cin hanci domin lalata tuhumar da ake yiwa mataimakin shugaban kasar William Ruto na aikata laifuffukan yaki.
Kotun ta kuma bayyana neman wasu Karin mutane biyu Philip Kipkeoch Bett da Walter Barasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu