Tanzania

Shugaban Tanzania John Magufuli yasaha rantsuwar kama aiki

Shugaban kasar Tanzania John Magufuli
Shugaban kasar Tanzania John Magufuli AP Photo

Shugaban Kasar Tanzania John Magufuli ya bukaci hadin kan al’ummar kasar bayan ya sha rantsuwar kama aiki domin yin wa’adi na biyu a zaben da Yan adawa suka yi zargin an tafka magudi.

Talla

Magufuli ya bayyana cewar yanzu an kamala zabe sai shirin yiwa kasa aiki, a jawabin da yayi yiwa dubban magoya bayan sa a filin wasan kasar, inda yace yanzu abinda ke gaban jama’ar kasar baki daya shine gina kasar su tare.

Shugaban ya sha alwashin mutunta ratsuwar da ya sha da kuma aiwatar da manufofin Jam’iyyar sa ta Chama Cha Mapinduzi.

Yan adawar kasar dai sun bukaci gudanar da zanga zanga a titunan kasar domin nuna rashin amincewar su da sakamakon zaben wanda ya nuna cewar Magufuli ya samu kashi 84 da kuma lashe kashi 97 na kujerun majalisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.