Uganda

Uganda ta tsayar da ranar zaben shugaban kasa

Hukumar zabe a kasar Uganda ta bayyana ranar 14 ga watan Janairu a matsayin ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa wanda shugaba Yoweri Museveni zai fafata da wasu 'yan takara 10 cikin su harda Bobi Wine.

Shugaban kasar Uganda Yuweri Museveni.
Shugaban kasar Uganda Yuweri Museveni. Ug.gov
Talla

Shugaban hukumar zaben Paul Bukenya ya sanar da ranar a sakon da ya aike ta kafar twitter, yayin da ya ke gayyatar daukacin 'yan takarar da su halarci wani taron da Hukumar sa za ta yi da su.

Tuni dai Hukumar ta ce 'yan takara 11 suka gabatar da takardun su aka kuma tantance su, cikin su harda shugaba Yoweri Museveni mai shekaru 76 da ke neman wa’adi na 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI