Turai

Macron ya lashi takobin tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Eric Gaillard/Pool via AP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya lashi takobin tsaurara matakan tsaro a kan iyakoki Faransa bayan jerin hare-haren da aka kaddamar a kasar da suka hada da harin wuka a Majami’ar birnin Nice wanda wani dan ci-ranin Tunisia ya kai.

Talla

A yayin wata ziyara da ya kai kan iyakar Faransa da Spain, shugaba Macron ya kuma yi kira da a samar da sauye-sauyen bada fasfo na kasashen Schengen a Turai.

Macron wanda ya samu rakiyar Ministan cikin gida Gerald Darmani da Ministan kula da lamuran Turai Clement Beanue, ya ce, zai gabatar da kudirin tsaurara matakan tsaro kan iyaka a taron da Kungiyar Tarayyar Turai za ta gudanar a cikin watan gobe.

Shugaban na Faransa ya ce, kudirin nasa zai kunshi karfafa tsaro kan iyakoki, inda kuma jami'an ‘yan sanda za su ci gaba da sanya ido.

Macron ya kara da cewa, Faransa za ta rubanya jami’an tsaron ta da ta jibge a kan iyakokinta da kasashen Turai zuwa dubu 4, 800 daga 2,400 saboda tsanantar barazanar ta’addanci.

A makon jiya Faransa ta shiga cikin gagarumin shirin ko-ta-kwana bayan an kashe mata mutane uku ta hanyar daba musu wuka a Majami’ar birnin Nice, harin da ake kallo a matsayin na mayaka masu ikirarin jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.