Kamaru

An gudanar da jana’izar daliban da Yan bindiga suka hallaka a Kumba

Makarantar Kumba da yan bindiga suka kai hari tareda kashe dalibai
Makarantar Kumba da yan bindiga suka kai hari tareda kashe dalibai REUTERS/ Josiane Kouagheu

Dubban Mutane ne suka halarci jana’izar daliban makarantar da Yan bindiga suka hallaka a Kumba dake Yankin da ake fama da matsalar Yan aware a kasar Kamaru.

Talla

Cikin mutanen da suka halarci jana’izar harda Firaministan Kamaru Joseph Dion Ngute wanda ya sha alwashin ganin jami’an tsaro sun kamo wadanda suka aikata kisan an kuma hukunta su.

A ranar 24 ga watan Oktoba ne Yan bindiga suka kai hari makarantar Mother Francisca inda suka harbe dalibai guda 7 har lahira, abinda ya gamu da mummunar suka daga ciki da wajen Kamaru.

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Afirka duk sun yi Allah wadai da harin wanda suka bayyana shi a matsayin abin takaici da kuma tada hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.