Najeriya

Kotu ta amince da nadin Amb Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19

Babbar Kotun Jihar Kaduna dake Zaria ta yanke hukuncin cewar Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ne zababben Sarkin Zazzau na 19, yayin da tayi watsi da karar da Iyan Zazzau Bashar Aminu ya shigar domin kalubalantar nadin da gwamnatin Jihar Kaduna ta masa.

Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli sarkin Zazzau
Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli sarkin Zazzau YouTube
Talla

Mai shari’a Kabir Dabo ya bada umurnin ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai da ya gudanar da bikin nadin Sarkin ranar litinin 9 ga wannan wata.

Idan dai ba’a manta ba Gwamnatin Jihar Kaduna dake Najeriya ta sanar da nadin Amb Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin Sarki na 19 domin maye gurbin Dr Shehu Idris Sarkin Zazzau na 18 da Allah ya yiwa rasuwa.

Sabon Sarkin Zazzau ya fito ne daga gidan Sarautar Mallawa wadanda rabon su da hawa karagar mulki aka kwashe shekaru 100 a cikin wannan wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI