Afrika

Kotun hukunta manyan laifuka ta Duniya na neman yan Kenya 2

Fatou Bensouda,Babbar Mai Gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuffuka dake Haque
Fatou Bensouda,Babbar Mai Gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuffuka dake Haque EVA PLEVIER / ANP / AFP

Babbar Mai Gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuffuka dake Haque Fatou Bensouda ta bukaci gwamnatin Kenya da at mika mata mutane 2 da ake zargi da lalata shaidun da ake da su a shari’ar laifuffukan yakin da ake tuhumar wasu yan siyasar kasar, bayan wani shaida guda ya gabatar da kan sa.

Talla

Wani lauyan kasar Paul Gicheru ya gabatar da kan sa ga kotun ranar litinin kuma ana sa ran ya gurfana a gaban alkalai domin amsa tuhuma dangane da lalata shaidun wannan juma’ar.

Za’a tuhumi Gicheru da laifin baiwa shaidu guda 6 cin hanci domin lalata tuhumar da ake yiwa mataimakin shugaban kasar William Ruto na aikata laifuffukan yaki.

Kotun ta kuma bayyana neman wasu Karin mutane biyu Philip Kipkeoch Bett da Walter Barasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.