Nijar-Faransa

Shugaba Issoufou ya gana da Le Drian a Yamai

Ministan harakokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian a jiya alhamis ya gudanar da wata ziyara a Nijar, ya kuma yi amfani da wannan dama wajen ganawa da shugaba Mahamadu Issoufou, inda suka tattauna a kan batutuwa da dama da suka hada da  batun yaki da ta'addanci a yankin Sahel. 

Jean-Yves Le Drian.
Jean-Yves Le Drian. REUTERS/Paul Lorgerie
Talla

A shekara mai kamawa ne ake gudanar da zaben shugabancin kasar Nijar,Ministan harakokin wajen Faransa ya jaddada goyan bayan kasar wajen tallafawa Nijar  a zantukan da suka jibanci tattalin arziki, tsaro da sauren su

Le Drian ya karasa da cewa Faransa za ta bayar da hadin kai don gannin an cimma zaman lafiya kafin zabe dama bayan sa,tareda baiwa yan Nijar damar gudanar da zabin dan siyasar da ya dace ya shugabanci kasar bayan zabe cikin adalci da gaskiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI