Amurka

Ba'a kammala tattance sakamako ba tukuna-Trump

Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump
Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump Brendan Smialowski / AFP

Tsohon Mataimakin shugaban Kasar Amurka joe Biden ya lashe zaben shugaban kasar da akayi ranar talata, sakamakon lashe kujerun wakilai 273 da ake bukata ga duk dan takarar da ake bukata yayi nasara.

Talla

Kafofin yada labaran Amurka da suka hada da CNN da NBC da CBS duk sun ruwaito cewar nasarar da Biden ya samu a Pennsylvania ta bashi damar zama zababben shugaba da kuma kawo karshen mulkin shugaba Donald Trump.

Alkaluma sun nuna cewar Biden shugaban da ya samu kuri’u sama da miliyan 74 a tarihin Amurka.

Rahotanni sun ce mutane kusan miliyan 160 suka kada kuri’u a zaben na Amurka, wanda ya rarraba kan Amurkawa sakamakon rawar da gwamnatin shugaba Donald Trump ta taka musamman wajen tinkarar cutar korona wadda ta kasha mutane sama da 230,000.

Samun nasara a Jihohin Pennsylvania da Michigan da Wisconsin wadanda dama jihohin da Yan Democrat ke samun nasara ne ya sa Biden ya samu kujerun wakilai 273 daga cikin 538 da ake da su a Amurka baki daya.

Rahotanni sun ce Biden zai fuskanci matsala a Majalisar Dattawa wanda Yan Republican ke cigaba da samun rinjaye, yayin da Yan democrat suka rike Majalisar wakilai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.