Cote d'Ivoire

An kama jagoran jam'iyyar adawa a Ivory Coast

Jam’iyyar adawa ta kasar Ivory Coast ta ce hukumomin kasar sun kama daya daga cikin jagorointa, Pascal Affi N'Guessan wanda ya tsere bayan da ya yi watsi tare da nuna kin amincewa da sake zaben Alassane Ouattara don yin wa’adi na 3 a matsayin shugaban kasar.

Pascal Affi N'Guessan, dan takaran jam'iyyar adawa a Ivory Coast.
Pascal Affi N'Guessan, dan takaran jam'iyyar adawa a Ivory Coast. Luc Gnago/Reuters
Talla

Ouattara ya lashe zaben shugaban kasar da ggarumin rinjaye bayan da masu adawa da burinsa suka yi kira da a kaurace wa zaben, suna mai zarginsa da zarce ka’ida, lamarin da ya janyo rikicin siyasa a kasar.

Wani dan jam’iyyar adawa ta Ivorian Popular Front Eddie Ane, ya ce an kama Affi N'Guessan a cikin dare a garin Bongouanou da ke tsakiyar gabashin kasar.

N'Guessan, wanda tsohon Firaministan kasar ne, shine kakakin jam’iyyar adawa, kuma dan takara a zaben shugaban kasar na 31 ga watan Oktoba.

Akalla mutne 40 aka kashe a tarzomar da ta tashi sakamakon adawa da neman wa’adin mulki na 3 da shugaba Ouattara ke yi, abin da y tada fargabar cewa kasar na iya fadawa cikin irin rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutane dubu 3 a shekarar 2010.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI