Afrika

Kotu ta amince da zaben Alpha Conde

Alpha Condé Shugaban kasar Guinee
Alpha Condé Shugaban kasar Guinee RFI

Kotun dake fassara kundin tsarin mulki a kasar Guinea ta amince da nasarar da shugaba Alpha Conde ya samu a zaben shugaban kasar da aka yi makon jiya wanda zai bashi damar yin wa’adi na 3.Alkalan kotun sun yi watsi da kalubalantar sakamakon zaben da shugaban yan adawa Cellou Dalein Diallo ya gabatar, bayan ya samu kashi 33 da rabi, sabanin kashi 59 da rabi da shugaba Conde ya samu.

Talla

Diallo ya shaidawa kotun cewar alkaluman da wakilan sa suka tattara a tashoshin zabe sun nuna masa cewar shi ya samu nasara.

Yayin da wakilan kungiyar kasashen Afirka da na ECOWAS suka amince da sahihancin zaben, kasar Faransa da kungiyar kasashen Turai da kuma Amurka sun bayyana shakku game da sakamakon.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun mamaye gidan sa kafin gabatar da matsayin kotun, yayin da yan Sanda kwantar da tarzoma suka tare hanyar zuwa gidan sa domin hana shi ganawa da manema labarai.

Da wannan hukunci na kotu, yanzu shugaba Conde mai shekaru 82 ya kama hanyar yin sabon wa’adi da kuma damar sake takara idan ya kamala saboda sauya kundin tsarin mulkin da yayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.