Najeriya: Gwamnati za ta rufe asusun ajiyar masu goyon bayan EndSARS

A Najeriya, wata Babbar kotu a Abuja ta baiwa babban bankin kasar damar dakatar da asususn ajiyar banki na hukumomi da daidaikun mutane da ke da nasaba da masu zanga zangar kin jinin cin zalin da ‘yan sandan ke yin a EndSARS kamar yadda ya bukata.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Najeriya
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Najeriya Temilade Adelaja/Reuters
Talla

Babban bankin na Najeriya ya mika wannan bukata ce a ranar 20 ga watan Oktoba, kuma kotu ta umurci bankuna da wadannan mutane ko kamfanonin ke hulda da su da su dakatar da asusun ajiyarsu har zuwa lokacin da baban bankin kasar zai kammala bincike a kan wadannan asusun ajiya.

Zanga zangar adawa da cin zalin da ‘yan sanda ke yi da wasu matasa suka shirya kasar a watan da ya gabata ta yi sanadin tarzoma da t janyo asarar rayuka da dukiyoyi a wasu sassan kasar, lamarin da ya kada hantar hukumomi.

A sassa da dama na jihohin kudanci da arewacin kasar, an samu matsalar farfasa gidajen ajiyar abincin gwamnati da wasu suka yi suna ta dibar kayan abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI