Amurka

Shugabannin Duniya sun fara mayar da martani kan nasarar Joe Biden

Shugabannin kasashen duniya sun fara aikewa da sakon taya murna ga zababben shugaban Amurka Joe Biden wanda ya kada shugaba Donald Trump dake rike da mulkin kasar.

Zababben shugaban  Amurka Joe Biden
Zababben shugaban Amurka Joe Biden Studio Graphique FMM
Talla

Firaministan Canada Justin Trudeau ya taya zababben shugaban murna tare da mataimakiyar sa Sanata Kamala Harris inda yace yana fatar yin aiki tare da su da kuma gwamnatin su wajen magance matsalolin da suka addabi duniya.

Firaministan Ireland Michael Martin ya bayyana Joe Biden a matsayin abokin kasar sa inda kakannin sa suka fito, yayin da yake cewa Biden ya dade yana kawance da kasar, kuma suna fatar yin aiki tare.

Ita ma gwamnatin Jamus ta bayyana nasarar Biden a matsayin wadda zata bude kofar kulla dangantaka mai karfi tsakanin Amurka da kasashen dake tsallaken kogin Atlantic.

Shugaban Jam’iyyar Labour a Birtaniya Keir Starmer ya bayyana nasarar Joe Biden a matsayin fata mai kyau da kuma hadin kai a maimakon rashin gaskiya da rarrabuwar kawuna.

Firaministan Scotland Nicola Sturgeon ta aike da sakon taya murna ga zababben shugaban Biden da kuma mataimakiyar sa Kamala Harris.

Firaministan Birtaniya aminin Donald Trump ya aike da sakon taya murna ga Joe Biden,kazalika Shugaban Faransa Emmanuel Macron shima ya aike da sakon taya murna ga Joe Biden da Sanata Kamala Harris.

Shima Magajin garin Birnin London Sadiq Khan ya bayyana nasarar Biden da Kamala Harris a matsayin abinda ya dace, inda ya bukaci sake kulla huldodin dangantaka sabanin gina Katanga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI