Amurka

Trump ya shiga cikin jerin shugabannin Amurka masu wa'adi guda

Nasarar Joe Biden a zaben shugaban kasar Amurka ta sanya shugaba Donald Trump cikin jerin sunayen shugabannin da suka gaza wajen samun wa’adi na biyu a tarihin Amurka.

Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump
Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump AP Photo/Alex Brandon
Talla

Tun bayan yakin Duniya na 2, shugabannin biyu kawai suka gaza wajen samun wa’adi na biyu da suka hada da Jimmy Carter da kuma George H.W. Bush, wato mahaifin shugaba George W Bush, sai kuma yanzu shugaba Donald Trump.

Masu sharhi sun zargi Trump da kama karya da sanya kan sa a gaba maimakon Amurkawar da suka zabe shi da salwantar da rayukan Amurkawa sama da 230,000 da suka mutu sakamakon cutar korona wanda shugaban ya gaza daukar mataki akai.

A karkashin mulkin Trump, Amurka tayi watsi da kawayen ta na kasashen duniya musamman kasashen Turai, wadanda shugaban ya dinga cacakar su a karkashin shirin sa da yake kira Amurka a farko, yayin da aka samu rarrabuwar kawunan Amurkawa musamman bakake da farare a cikin kasar.

Shugaban mai barin gado yayi ta takun saka da Majalisar Dinkin Duniya wajen bata kudade da kuma aikin da take yi da Hukumar Lafiya ta Duniya kan batun cutar korona da kuma kasashen NATO da ya zarga da kin bada kudade.

Shugaba Trump ya kuma fitar da Amurka daga cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran da yarjejeniyar sauyin yanayin Paris da kuma sake fasalin Gabas ta Tsakiya a rikicin da ake tsakanin Falasdinawa da Israila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI