Amurka

Jaridun Duniya sun yi murna da faduwar Trump

Kafofin yada labaran Duniya sun bayyana farin cikin su da shan kayen da shugaba Donald Trump yayi a zaben Amurka, yayin da suka fara mayar da hankali kan kalubalen dake tattare da manufofin kasar.

Jaridun Duniya sun yi murna da faduwar Trump
Jaridun Duniya sun yi murna da faduwar Trump AP Photo/Sunday Alamba
Talla

Jaridar Independent da ake wallafawa a Birtaniya, ta yiwa taken sharhin ta ‘Sabon babi a Amurka’ inda ta wallafa hotan Biden kusa da Harris da kuma nuna gagarumar nasarar da ya samu.

Jaridar Sunday Times ta wallafa hotan wata bakar fata nade da tutar Amurka da kuma taken, ‘ Biden mai bacci ya tashi Amurka’ a matsayin wani shagube ga shugaba Trump kan yadda yake sukar Biden.

Ita kuwa Jaridar Observer ta wallafa cewar, ‘Joe Ne’ tare da hotan sa yana murmushi a shafin farko.

Jaridar Bild ta Jamus ta wallafa hotan Trump da taken ‘Ficewa ba tare da mutunci ba’.

Jaridar Sueddeutsche Zeltung ta wallafa cewar, ‘Amurka sun samu ‘yanci, sun samu sauki’, yayin da take cewa Biden ya gaji shugabanci mai nauyi sabanin shugabannin da suka gaba ce shi.

Daily Telegraph ta Australia da Rupet Mudoch ya mallaka ta mayar da hankali ne kan jajircewar da shugaba Trump yayi na kin amincewa da sakamakon inda take cewa, ‘Abokin gabar da ake ganin bashi da nauyi, ya samu nasarar yaki’.

Suma jaridun Iran sun yi sharhi da dama kan faduwar Trump, wanda suka bayyana shi a matsayin ‘babban makiyi’, yayin da wata jaridar tace ‘Makiyin bayyane ya tafi, na boye ya zo’.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI