Najeriya

Mun gaji da barazanar raba Najeriya - Dattawan Arewa

Shugabannin da suka fito daga Yankin Arewacin Najeriya sun bukaci shugabannin kungiyoyin kabilun da suka fito daga shiyoyin kudancin kasar da su daina yi musu barazanar sake fasalin Najeriya ko kuma darewar kasar zuwa kasashe daban daban.

Alhaji Tanko Yakasai.
Alhaji Tanko Yakasai.
Talla

Bayan wani taro na Gwamnoni da Yan siyasar da suka fito daga Yankin, shugabanni sun ce sun gaji da yadda kungiyoyi irin su Afenifere ta shugabannin Yarbawa da takwarorin su na Yan kabilar Igbo ke yi wa yankin barazanar ballewa muddin aka ki sake fasalin siyasar kasar kamar yadda suke bukata.

Tsohon Gwamnan Nasarawa Abdullahi Adamu ya ce wasu sun raina yankin arewacin Najeriya dangane da yadda ake tafiya yanzu, kuma sun gano yadda wasu ke kokarin yi wa wannan gwamnatin zagon kasa, abin da ya sa ya zama wajibi a tashi tsaye domin mayar da martani a kai.

Sanata Adamu ya ce arewacin Najeriya ne ginshikin da ya tabbatar da dayantakar kasar, kuma babu abin kunya wajen bayyana haka domin kare mutuncin shugaban da ke jagoranci yanzu, saboda idan ‘dan kudu ke mulki ba’a masa irin wannan cin fuska.

Shi ma tsohon dan siyasa Alhaji Tanko Yakassai ya bayyana cewar an shirya zanga zangar adawa da cin zarafin da 'yan Sanda ke yi ne domin durkusar da kasar da kuma rarraba ta.

Yakasai ya ce mutanen arewa suna amfani da lafuza masu taushi wajen cewar wasu bata gari suka karbe ragamar zanga zangar amma a hakika dama haka aka shirya ta domin rarraba Najeriyar.

A martanin da ta yi tsohuwar mataimakiyar gwamnan Lagos kuma daya daga cikin shugabannin kungiyar Yarbawa ta Afenifere Kofoworola Bucknor-Akerele ta bayyana bacin ran ta da taron shugabannin arewacin Najeriyar inda take cewa abin da zai tabbatar da dorewar Najeriya shine mayar da mulkin kasar yankin kudu a shekarar 2023.

Bucknor Akerele ta ce bukatar su ta safe fasalin Najeriya ya ma zarce na mika musu mulki a shekarar 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI