WHO-Lafiya

Mutane sama da milyan 50 suka kamu da cutar Korona

Asibitin kula da masu dauke da cutar covid 19
Asibitin kula da masu dauke da cutar covid 19 iStock / Morsa Images

Hukumar Lafiya ta Duniya tace adadin mutanen da suka harbu da cutar korona sun zarce miliyan 50 yanzu haka a fadin duniya, sakamakon alkaluman da aka tattara bayan yiwa jama’a gwaji.

Talla

Alkaluman da Hukumar ta gabatar sun ce tun bayan barkewar cutar a watan Disamba an samu mutane miliyan 50 da dubu 10,400 da suka harbu da ita, yayin da miliyan guda da dubu 251,980 suka mutu.

Hukumar tace a nahiyar Turai kawai an samu mutane sama da miliyan 12 da rabi da suka harbu, kuma mutane sama da 305,000 sun mutu, sai kuma yankin Kudancin Amurka da Carribean da aka samu mutane sama da miliyan 11 da rabi da suka harbu, kuma 411,000 sun mutu, sannan nahiyar Asia mai mutane miliyan 11, kuma 177,000 sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.