Sojin Faransa sun kashe 'yan ta'adda 10 a Mali

Sojojin Mali yayin wani atisaye  a Gao.
Sojojin Mali yayin wani atisaye a Gao. REUTERS/Luc Gnago

Rundunar Sojin Faransa dake yaki da 'yan ta’adda a yankin Sahel ta sanar da kashe mayakan dake alaka da kungiyar Al Qaeda 10 a wani hari da ta kai musu a kasar Mali.

Talla

Kakakin rundunar Kanar Frederic Barbry ya ce dakarun nasu sun kaddamar da hare hare ne tun ranar juma’a a kauyen N’Tillit dake da nisar kilomita 80 daga birnin Gao inda sansanin rundunar Barkhane take.

Jami’in yace an dauki hotunan mayakan ne ta hanyar amfani da jirgin sama mai sarrafa kansa wanda aka yi amfani da shi wajen kai musu hari da kuma rakiyar jiragen sama biyu masu saukar ungulu.

Kanar Barbry ya ce babu wani sojan su da ya samu rauni a harin, yayin da suka kama mutane biyu da ran su.

Ko a ranar litinin rundunar ta Barkhane ta ce sojojinta sun kashe mayaka sama da 50 dake alaka da kungiyar Al Qeada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.