Habasha

Fira ministan Habasha ya kori babban hafsan tsaronsa kan rikicin Tigray

Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed.
Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed. © Tiksa Negeri / REUTERS

Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed ya kori babban hafsan rundunar sojin kasar Janar Adem Mohammed, inda ya maye gurbinsa da mataimakinsa Berhanu Jula.

Talla

Matakin Fira Ministan Habashan na zuwa ne bayan jikkatar adadin dakarun kasar mai yawa a fadan da suka shafe kwanaki akalla 6 suna gwabzawa da ‘yan tawaye arewacin yankin Tigray.

Zalika bayaga ga korar babban hafsan tsaron sojin kasar, Fira Ministan Habashan ya kuma kori manyan mukarrabansa da suka hada da shugaban rundunar yan sandan kasar, da ministan harkokin wajen sa, sai kuma nada shugaban yankin Amhara a matsayin sabon shugaban hukumar leken asirin Habasha.

Yanzu haka dai firaminista Abiy Ahmed na cigaba da yin kira ga kasashe da sauran hukumomin kasa da kasa da fahimci cewar farmakin sojin da ya bada umarnin kaddamarwa kan jam’iyyar TPLF dake mulkar yankin Tigray, ya yi ne da kyakkyawar manufa, sakamakon aniyar jam’iyyar ta neman wargaza kasa.

Fira Ministan Habashan ya kara da cewar jam’iyyar ta TPLF, ta dauki nauyin horas da mayakan sa kai masu yawan gaske gami da basu makamai domin rusa gwamnatin Habasha ta hanyar haddasa yaki.

Tuni dai Fafaroma Francis ya shiga jerin shugabanni daga sassan duniya dake fargabar barkewar yakin basasa a Habasha, inda ya bukaci gwamnatin kasar ta rungumi zabin tattaunawa da addu’a a maimakon amfani da karfin soji.

Shi kuwa shugaban yankin Tigray dake cikin tashin hankalin Debretsion Gebremichael kira yayi ga kungiyar kasashen Afrika da ta yi amfani da karfin ikonta wajen kare kasar Habasha daga fadawa kazamin yakin basasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.