Ivory Coast

Zaben Ivory Coast: Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Alassane Ouattara

Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara
Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara REUTERS/Luc Gnago/File Photo

Kotun Kolin Cote d’Ivoire ta tabbatar da sakamakon zaben da aka yiwa shugaba Alassane Ouattara domin yin wa’adi na uku bayan zaben da ya gudana ranar 31 ga watan jiya wanda yan adawar kasar suka kaurace masa.

Talla

Shugaban alkalan kotun Mamadou Kone ya bayyana amincewa da sakamakon zaben da ya gudana ranar 31 ga watan Oktoba, inda yake cewa babu wasu matsaloli da aka samu da suka shafi kimar zaben.

Hukumar zaben kasar ta bayyana cewar shugaba Alassane Ouattara mai shekaru 78 ya samu sama da kasha 94 na kuri’un da aka kada, bayan da shugabannin yan adawa suka bukaci magoya bayan su da su kauracewa zaben.

Akalla mutane kusan 50 aka kasha a tashe tashen hankulan da suka biyo bayan takarar Ouattara tun daga watan Agusta, abinda ya jefa fargabar cewar kasar na iya fuskantar irin tashin hankalin da aka gani a shekarar 2010 wanda yayi sanadiyar kasha mutane kusan 3,000.

Rahotanni sun ce harkokin yau da kullum sun fara komawa kamar yadda aka saba a Abidjan, yayin da aka tsare tsohon Firaministocin kasar Pascal Affi N’Guessen da Maurice Kakou Guikahue, mataimakin shugaban Jam’iyyar Henri Konan Bedie.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.