Mali

Tsohon shugaban Mali Amadou Toure ya rasu yana da shekaru 72

Tsohon shugaban Mali Amadou Toumani Toure da ya taimaka wajen tabbatar da dimokiradiya a Yankin Sahel ya rasu yana da shekaru 72 a duniya.

Tsohon shugaban Mali, marigayi Amadou Touani Touré.
Tsohon shugaban Mali, marigayi Amadou Touani Touré. AFP/Michele Cattani
Talla

Wani dan uwansa, Oumar Toure ya sanar da rasuwar tsohon shugaban a Turkiya inda aka kai shi domin kula da lafiyarsa.

Wani likita a Bamako ya bayyana cewar an yiwa tsohon shugaban dashen zuciya a wani asibiti dake Luxembourg kwanakin baya, kuma ya samu lafiya, amma daga bisani sai aka dauke shi zuwa Turkiya inda Allah ya masa rasuwa.

Toure wanda tsohon soja ne, ya taimaka wajen kifar da gwamnati Moussa Traore a shekarar 1991, bayan shugaban yayi kane- kane a mulki tun daga shekarar 1968, inda ya jagoranci gwamnatin rikon kwarya, ya kuma shirya zaben da Alpha Oumar Konare ya lashe a shekarar 1992, ya kuma zama zababben shugaban Mali na farko bayan samun ‘yancin kan kasar.

Tsohon shugaban da ake yi wa lakabi da ATT, ya zama shugaban kasa a shekarar 2002 kana ya sake lashe zabe a shekarar 2007, kafin shima a kifar da gwamnatin sa a shekarar 2012 abinda ya jefa Mali cikin rikicin siyasa da kuma boren Yan Tawaye.

Kawar da shi daga karagar mulki da sojojin da suka yi bore suka yi, ya baiwa mayakan jihadi damar mamaye arewacin kasar da kuma yunkurin kafa kasa ta kan su, har zuwa lokacin da sojojin Majalisar dinkin Duniya da na Faransa suka taka musu birki, daga bisani kuma aka kafa rundunar G5 Sahel domin yakar su.

Wannan rikici yayi sanadiyar mutuwar dubban mutane, yayin da wasu dubban suka tsere suka bar gidajensu.

Daga cikin sojojin da suka kawar da Toure daga mulki har da Kanar Malick Daw, mataimaki na 2 na gwamnati mai ci, wadanda aka tilasta wa shirya zabe a cikin watanni 18.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI