Afrika

Mutanen Habasha 11,000 suka tsallaka zuwa Sudan

Hukumomin kasar Sudan sun ce akalla yan kasar Habasha 11,000 suka tsallaka zuwa kasar su domin kaucewa tashin hankalin dake gudana a Tigray.

Wasu daga cikin yan Habasha kan hanyar su ta zuwa Sudan
Wasu daga cikin yan Habasha kan hanyar su ta zuwa Sudan REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana taimakawa wadannan yan gudun hijira 7,000, yayin da yawan su ke dada karuwa.

Firaministan Sudan Abdalla Hamdok ya bukaci kawo karshen fadan da ake gwabzawa tsakanin sojojin gwamnati da mayakan Tigray lokacin da ya gana da ministan harkokin wajen Habasha Osman Saleh da ya ziyarce shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI