Najeriya

Hukumomin Najeriya za su kara farashin fetur zuwa N170 duk lita

‘Yan Najeriya za su bukaci yin damarar fuskantar wani karin farashin man fetur da     dangoginsa a ‘yan kwanaki masu zuwa, kamar yadda rahotanni da ke fitowa daga kasar ke tabbatarwa.

Wani gidaan mai a Lagos,Najeriya (a matsayin misali)
Wani gidaan mai a Lagos,Najeriya (a matsayin misali) PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Talla

Hakan zai auku ne saboda kwaskwarimar da hukumar kayyade frashin albrkatun man nfetur ta kasar ta yi wa farashin man daga inda ake dakonsa, inda yanzu litar fetur ta tashi daga N147.87 zuwa N155.17 a wajen dakonsa.

Hukumar dai wani bangare ne a karkashin kamfanin man fetur na kasar NNPC, kuma a yanzu haka daga kasashen waje take sayo dukkannin man fetur da ake amfani da su a kasar.

Wata sanarwa da jaridar Premium Times ta ce ta gani na nuni da cewa za a fara amfani da sabon farashin ne daga 13 ga wata Nuwamban nan.

Sanarwar wacce ta samu sa hannun Ali Tijani na PPMC na nuni da cewa yanzu farashin kawo man cikin kasar ya karu daga N199 a watan Satumba zuwa N123 a watan Nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI