Mohammed Salah ya kamu da coronavirus

Dan wasan gaba na Liverpool Mohammed Salah dan asalin Masar ya kamu da annobar korona.

Dan wasan Masar da Liverpool Mohamed Salah
Dan wasan Masar da Liverpool Mohamed Salah GEOFF CADDICK / AFP
Talla

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da Hukumar kwallon kafar kasar sa Masar ta wallafa ta shafinta na Intanet.

Sanarwar tace, dan wasan ya kamu da cutar ce yayin wani aikin kasa-da-kasa, kuma tuni aka sanar da kungiyarsa ta Liverpool halin da ake ciki.

Sanarwar Hukumar kwallon kafar Masar ta ce, dan wasan bai nuna wani alamu na rashin lafiya ba, amma kuma yanzu haka ya killace kansa kamar yadda dokoki suka tanadar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI