Habasha

Rikicin Habasha: Sudan ta karbi 'yan gudun hijira dubu 16

Hukumar kula da ‘Yan gudun hijira ta MDD ta karas da cewa yanzu haka akwai ‘yan kasar Habasha dake gudun hijira dubu 16 a kasar Sudan biyo bayan yakin da Habasha ta kaddamar a yankin Tigray. wasu ‘yan gudun hijiran sun sami isa sansanonin da aka ware masu ne a Sudan, bisa kekuna, wasu kuma taka sayyada suka yi.

Sudan ta karbi 'yan gudun hijira 16 daga Habasha
Sudan ta karbi 'yan gudun hijira 16 daga Habasha Reuters
Talla

Yawan ‘yan gudun hijiran daga Habasha dai sai karuwa yake yi, inda aka jibge su a wani sansani da aka taba jibge su a sherun 1980 a lokacin da ‘yan Habashan suka yi fama da matsanancin fari.

Aisir Khaled shugaban sansanin ‘yan gudun hijira na Kassala dake Sudan, yana ganin yadda ‘yan Habasha ke tururuwan zuwa sansanin , ya zuwa yau Juma’a aka sami ‘yan gudun hijira dubu 20.

Yawancin ‘yan gudun hijiran dai yara ne kanana, da mata da matasa dake neman kauracewa kazamin tarzoman da ake fafatawa na tsawon mako daya a kasar ta su.

Wasu ‘yan gudun hijiran a wahalce, kan rika hutawa a hanyarsu ta shiga kasar Sudan, bayan da suka yi tattaki zuwa wani kogi, dake tsakanin kasashen biyu.

A mako dayan da Sojan Habasha suka yi suna yakar al’ummar yankin Tigray, daruruwa suka yi hasarar rayukansu da kaddarori

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI