Habasha

MDD ta yi gargadi kan kazancewar aikata laifukan yaki a Tigray

Majalisar dinkin duniya ta yi gargadin yiwuwar tafka laifukan yaki a yankin Tigray na Habasha, inda a yanzu haka ake gwabza fada tsakanin sojojin kasar da kuma ‘yan tawayen da ke marawa jam’iyyar TPLF mai mulkin yankin da ta bijirewa gwamnati.

Wasu sojojin kasar Habasha yayin komawa sansaninsu da ke Danasha, a yankin Amhara region bayan fafatawa da 'yan tawayen (TPLF), a yankin Tigray.
Wasu sojojin kasar Habasha yayin komawa sansaninsu da ke Danasha, a yankin Amhara region bayan fafatawa da 'yan tawayen (TPLF), a yankin Tigray. Tiksa Negeri/Reuters
Talla

A makon jiya Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed ya bada umarnin kaddamar da farmakin soji kan mayakan sa kan na Tigray, bayada ya tuhumi shugabannin yankin da yunkurin haifar tashin hankali a kasar, ta hanyar daukar nauyin horas da mayaka tare da basu makamai.

A baya bayan nan kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International, ta ce an yiwa fararen hula masu yawa kisan gilla a yankin Tigray na Habasha mai fama da rikici.

Amnesty tace shaidun gani da ido sun dora alhakin kisan gillar kan dakarun ‘yan tawayen dake marawa jam’iyyar TPLF mai mulkin yankin na Tigray, da ta bijirewa gwamnatin Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI