Afrika

Hukumomin agaji na kasa da kasa sun bukaci gaggauta samar da tallafi zuwa Chadi

Yan gudun hijira na kasar Chadi
Yan gudun hijira na kasar Chadi PHILIPPE DESMAZES / AFP

Hukumomin agaji na kasa da kasa sun bukaci gaggauta samar da tallafi ga kimanin mutane dubu 11 da 500 da iftaila’in ambaliyar ruwa ya tagayyara a sassan N’Djemena, babban birnin kasar Chadi. 

Talla

Tun cikin watan Agusta ambaliyar ruwan ta raba dubban mutanen da muhallansu dake kudancin birnin na N’Djemena, sakamakon tumbatsar da kogin Chari yayi, wanda ya dangane da Tafkin Chadi.

Kogin Chari da ya ratsa Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, da Kamaru zuwa kuma cikin Chadi, daya ne daga cikin manyan idanun ruwan Tafkin Chadi.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya IOM, ta ce yanzu haka wadanda ambaliyar ta shafa na cikin tsananin bukatar tantuna, magunguna da abinci da kuma ruwan sha mai tsafta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.