Muhallinka Rayuwarka

Kungiya ta masu nomawa da sarrafa tattasai da kayan yaji a Najeriya

Sauti 18:57
Tattasai da kayan yaji daga gona
Tattasai da kayan yaji daga gona © Mercedes Ahumada

Tattasai da sauran dangin kayan yaji abubuwa ne da ake sarrafawa wajen amfani ta hanyoyi masu yawa baya ga kasancewarsu abin ci, inda ake amfani da su wajen sarrafa magunguna da dai sauransu.Binciken da sashin samar da abinci da bunkasa noma na bankin duniya ya gudanar ya nuna cewa Najeriya tafi kowace kasa samar da tattasai da kayan yaji a gaba daya yankin kasashen Afrika masu yanayi na zafi, inda tace Najeriya tana samar da ton dubu 715 a filin noma da ya kai girman hekta dubu 90,000.Nura Ado Suleiman ya mayar da hanakali tareda duba alfanun dake cikin irin kungiya.